
Jami’an lafiya 3 da wani mara lafiya ne suka rasu sakamakon bullar cutar da ake zargin zazzabin Lassa ce ta zama sanadi a babban asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna.
Wata majiya a asibitin ta ce daga cikin jami’an lafiyan da suka rasu har da wata mai yiwa kasa hidima NYSC da ta ke aiki a asibitin sojojin.
Karin labari: An yankewa Adawale da wasu mutane 5 hukuncin rataya a jihar Ondo
Wata sanarwa da mukaddashin kwamandar sashen kiwon lafiya na rundunar sojin kasa ta Najeriya, Birgediya S.O Okoigo ta ce, wasu karin mutane ma kwance cikin mawuyacin hali a sakamakon zazzabin Lassa da ake zargi.
Cikin sanarwar “jami’an lafiyar sun rasu ne a garin jinyar mara lafiyan da ake zargi da cutar, a tsawon kwanaki 10 da suka wuce, inda ya nuna alamar cutar kafin daga bisani rai ya yi halinsa.
Karin labari: NLC ta jaddada shirin gudanar da zanga-zanga duk da barazanar DSS
An rufe sashen kula da lafiya na gaggawan domin kashe kwayoyin cutar, sannan an tsaurara matakan kariya domin hana yaɗuwarta, an tura samfurin kwayar cutar zuwa cibiyar gwajin kwayar cuta ta hukumar hana yaduwar cututtuka ta Kasa NCDC da ke Kano, domin gudanar da bincike” in ji sanarwar.
An gayyato jami’an tantance kwayar cuta na gwamnatin jihar Kaduna domin gudanar da bincike sannan an dauki matakan kariya domin takaita yaduwar cutar, haka zalika za’a samar da alluran riga-kafi domin dakile yaduwar wannan cuta kamar yadda bayanan sanarwar su ka nuna.











































