Dan-majalisar jihar Oyo ya mutu yana mai shekaru 46

Ademole Olusegun 750x430 1
Ademole Olusegun 750x430 1

Mai bawa shugaban majalisar jihar Oyo shawara kana al-amuran yada labarai, Oyekunle Oyetunji, ya tabbatar da rasuwar dan-majalisar jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola yau Laraba.

An tattaro bayanan cewa Popoola ya rasune bayan yasha fama da ciwoon hanta da kuma koda, wanda ya kai ga kwanciya a asibitin UCH na Ibadan.

Gwamnan jihar ta Oyo  Seyi Makinde , ya bayyana mutuwar dan majalisar a matsayin babban rashi ga jihar baki daya.

An zabi dan majalisar a shekarar 2019, a karkashin tutar jam’iyyar PDP.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here