Yadda muke siyan kaya da alat na bogi – Mutumin da ake zargin sa da damfara

images 13
images 13

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wani matashi mai shekara 45, mai suna Adewale Adesanya da laifin yin satar ta hanyar tura alat na banki na bogi domin damfarar ‘yan kasuwar POS da ‘yan kasuwa.

Adesanya, wanda aka kama shi da kwalabe guda hudu na giya shampain, Dom Perignom, wanda kowanne farashinsa ya kai Naira 117,900. ya tabbatar wa manema labarai cewa abokin aikinsa a wannan sana’ar ne ya horar da shi kan wannan damfara.

Ya ce sun sayi kayayyaki na miliyoyin naira ta hanyar amfani da alat na bogi da wasu aikace-aikace a wayarsu.

Wanda ake zargin ya ce ciniki na karshe da ya yi wanda ya fallasa shi kusan Naira 185,000 ne inda ya damfari wani ma’aikacin POS a Ibadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here