Shugaban Sri Lanka ya tsere daga kasar a jirgin sojoji  

Untitled 1 Recovered 8
Untitled 1 Recovered 8

Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga Sri Lanka a jirgi sama na yaki, a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.

Rundunar sojin sama ta kasar ta tabbatar da cewa shugaban kasar, mai shekara 73, ya tsere zuwa Maldives tare da matarsa da jami’an tsaro biyu.

Tserewar da Mr Rajapaksa ya yi daga kasar ta kawo karshen mulkin da iyalansa suka kwashe fiye da shekaru ashirin suna yi a kasar Sri Lanka.

Shugaban kasar ya buya bayan da dandazon jama’ar da ke zanga-zanga suka mamaye gidansa ranar Asabar, kuma ya yi alkawarin sauka daga mulki ranar Laraba, 13 ga watan Yuli.

Dan uwansa, wanda shi ne tsohon Ministan Kudin kasar Basil Rajapaksa, shi ma ya tsere daga Sri Lanka kuma an ce ya nufi Amurka.

Firaiministan Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar sannan aka sanya dokar hana fita a lardin da ke yammacin kasar, kamar yadda mai magana da yawunsa ya fada.

A yayin da ‘yan kasar Sri Lanka suka wayi gari da labarin tserewar shugaban kasar, dubban mutane sun bazama kan titunan Colombo, babban birnin kasar.

Da dama daga cikinsu sun taru a Galle Face Green, babban filin da ake gudanar da zanga-zanga a kasar.

A gefe guda kuma, hatsaniya ta kaure yayin da masu zanga-zangar suka yi yunkurin kutsa kai cikin ofishin firaiministan kasar da ke Colombo, sai dai sojoji sun hana su shiga.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here