Sojin Ghana ya mutu a aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu

Sojin, Ghana, mutu, aiki
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar wani sojan Mali guda a Sudan ta kudu da ke cikin dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ta...

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar wani sojan Mali guda a Sudan ta kudu da ke cikin dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ta yi fama da rikici tsawon shekaru.

Sanarwar da Majalisar ta fitar, ta ce Sojan na Ghana ya rasa ransa ne a yankin Abyei mai fama da rikici a iyakar kasar da Sudan.

Rahotanni sun ce rikici ya barke a sassa 3 na yankin Abyei tsakanin mayakan ‘yan tawaye masu rike da makamai da kuma jami’an tsaron da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Karanta wannan: Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota a Jihar Niger

A cewar sanarwar Majalisar baya ga Sojin akwai kuma tarin fararen hular da suka mutu, wanda ya tilasta kwashe mutane daga sassa 3 da rikicin ya tsananta zuwa tudun mun tsira.

Rikici tsakanin kabilun yankin na Abyei ba sabon abu bane lura da yadda suka shafe tsawon shekaru suna yakar juna a yankin wanda ke dauke da mabanbantan kabilu.

Yankin na Abyei mai arzikin albarkatun karkashin kasa, har yanzu ana takaddama game da hakikanin wanda ke da iko akansa tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here