Najeriya ita ma zata bi sahun sauran kasashen duniya wajen yin bankwana da shekarar 2023 tare da yin maraba da sabuwar shekarar 2024.
Kasar Kiribati da ke yankin Pacific it ace kasa ta farko da ta fara shiga sabuwar shekara ta 2024, yayin da agogon Najeriya ke nuna karfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
Karanta wannan: Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara wani asibiti a Jigawa
Bayan ita, kuma sai kasar New Zealand da ita ma ta shiga sabuwar shekarar 2024.
Ana kuma sa ran dubban daruruwan mutane za su halarci bukukuwan a faɗin duniya nan da sa’o’i masu zuwa domin nuna murnar shiga sabuwar shekara.
Mutane da dama na taruwa a birnin Sydney na kasar Australiya domin bikin wasan wuta na sabuwar shekara mai ban sha’awa a duniya.