Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Gwamna Yahaya Bello Na Jihar Kogi

Yahaya bello 2
Yahaya bello 2

Wasu miyagu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun farmaki ayarin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, yayin da yake hanyar komawa Lokoja daga birnin tarayya Abuja.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya raba wa ‘yan jarida ranar Asabar.

Ya ce wasu mutane da ake tsammanin magoya bayan Alhaji Muritala Yakubu Ajaka ne suka tare mai girma gwamna kana suka farmake shi da misalin karfe 12:30 na tsakar rana yau Asabar.

“Lamarin ya faru a kusa da sansanin sojin ruwa, kilomita kaɗan gabanin isa Lokoja kuma a wurin aka hangi ayarin Muritala Yakubu Ajaka, wanda daga ganin gwamna na zuwa suka tsohe hanyar.”

“Daga nan sai wasu ‘yan daba ɗauke da bindigogi suka buɗe wa ayarin mai girma gwamna wuta. Wasu daga cikin jami’an tsaro da hadiman da ke tare da ayarin gwamna sun ji raunuka.”

“Tuni aka garzaya da waɗanda suka rauni Asibiti domin kula da lafiyarsu. Muna kira ga ɗaukacin mutanen Kogi su kwantar da hankulansu yayin da jami’an tsaro suka bazama don kamo masu hannu a harin.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here