Sabon karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi alkawarin tabbatar da cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta ci gaba da mulki a Jihar Kano a zaben 2027 mai zuwa.
A yayin dawowarsa bayan an rantsar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar Asabar a Kano, Ata ya nuna godiyarsa game da nadin nasa tare da tabbatar da goyon bayansa ga jam’iyyar.
“Wannan nadin shi ne don mutanen Jihar Kano da Najeriya,” in ji shi. “Na tabbatarwa da Shugaba cewa, in Allah ya yarda, Jihar Kano za ta koma sansanin APC a 2027.”
Ya jaddada cewa nadin nasa yana da muhimmanci musamman ga yankin Kano Central, wanda yake da yawan masu kada kuri’a.
“Zan ci gaba da kasancewa a mazabata da yankin domin kara karfin jam’iyyarmu,” ya kara da cewa.
Ata ya bayyana shirin da zai yi na aiki tukuru don tabbatar da nasarar APC a Jihar Kano.
Ya jaddada muhimmancin kammala ayyukan da ake gudanarwa karkashin ma’aikatarsa, musamman wadanda suka danganci ajandar “Renewed Hope” na Shugaban kasa.
Har ila yau, ya nuna tabbaci ga iyawarsa na cika wadannan alkawura, yana mai fadin cewa gogewarsa a matsayin tsohon Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Kano da Shugaban Masu Rinjaye zai taimaka masa.
“Kano Central tana da mafi girman kuri’u. Tana da kashi 65% na masu rajistar zabe kuma babu wani babban mukami a can. Amma yanzu, shugaban kasa ya nada ni, kuma idan muka duba abin da suka ce, na kasance a Majalisar Dokoki tun daga 1999. Na taba zama kakaki, shugaban masu rinjaye, kuma mai ba wa gwamna shawara na musamman. Don haka muna da cikakken tabbaci na samun nasara a Jihar Kano.”