Sarkin Ibadan wato Olubada, Oba Saliu Adetunji ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.
Bayanai na cewa ya rasu ne a Asibitin University College (UCH) da sanyin safiyar Lahadi sakamakon rashin lafiya.
Oba Saliu Adetunji ya zama Olubadan a ranar 4 ga Maris, 2016 ne.
Ekarun Olubadan, Cif Amidu Ajibade ne ya tabbatar da rasuwarsa.