An bude sabon kantin sayar da magunguna mai suna suna 24 hours Best medix pharmacy, wanda ke aiki sa’o’i 24 don biyan bukatun al’umma na samun magunguna masu inganci a kowane lokaci.
Solacebase ta ruwaito cewa shagon yana kan hanyar Aminu Kano daura da mahadar Tal’udu.
Mallakin kantin Auwal Muhammad Lawan ya shaida wa Solacebase cewa bude sabon shagon maganin ya samo asali ne daga abin da ya gani a asibitinsa na Best Choice Hospital dake Sabuwar Gandu, inda marasa lafiya da ‘yan uwansu ke wahalar sayen magunguna da sauran kayayyaki da suka danganci kiwon lafiya.
Lawan ya ce kantin zai ringa gudanar da hada-hadar magunguna na tsawon awoyi 24 ga mazauna Kano.
A cewarsa baya ga wannan, kantin yana kuma sayar da kayan abinci, wanda suka hada da ‘ya’yan itatuwa, kayan marmari da sauran kayan masarufi na sa’o’i 24.
Dan kasuwar ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen magance yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasan da suka kai shekaru masu yawa.
Lawan ya lura da cewa, maganganu masu dadi da mutane suke yi kan shagon ya nuna cewa sabon kantin yana da makoma mai kyau a kasuwar Kano, domin kwastomomi sun yi ta tururuwa zuwa shagon tun daga lokacin da aka bude shi.
Wata kwastomar da aka zanta da ita yayin da take siyan kayan abinci a shagon ta ce ta sayi kayan sha, kayan tsafta da sauran kayan masarufi a farashi mai rahusa.













































