Kwankwaso ya karyata batun yin aiki don sake zaben Tinubu a 2027

Kwankwaso and Tinubu 1 750x430

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana aiki don sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2027, inda jaddada cewa ba shi da alaka da shugaban kasa ta fuskar siyasa.

Kwankwaso, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya karyata zargin yayin hirar da ya yi da Global TV a ranar Laraba.

Tsohon gwamnan ya mayar da martani ne kan maganganun Sanusi Bature, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf, wanda ya yi zargin a wani shiri a Arise TV cewa Kwankwaso yana goyon bayan burin Tinubu na wa’adi na biyu a boye.

Da yake mayar da martani kan zargin, Kwankwaso ya bayyana shi a matsayin karya, yana mai cewa mutane “marasa hankali kadai” ne za su yarda da hakan.

“Na yi imanin mutane marasa hankali ne kadai za su yarda da hakan, bama aiki wa kowa ba, muna aiki ne kawai ga NDC,” in ji shi.

Kwankwaso, ya kara da cewa ya yarda cewa akwai gangantaka a tsakaninsu, alaka mai kyau da Tinubu tsawon shekaru, amma ya jaddada cewa abota bai kamata a dauka a matsayin hadin gwiwar siyasa ba.

“Bola Tinubu babban yayana ne kuma abokina har yanzu, amma wannan ba yana nufin za mu hada dukkan ra’ayoyin siyasarmu da nasa ba.

Yana na shi, ni ma ina nawa,” in ji Kwankwaso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here