Gwamnatin tarayya ta amince da alawus na musamman ga farfesoshi da masu karatun gaba

Tunji Alausa

Gwamnatin tarayya ta amince da sabon alawus na shekara ga malaman jami’o’in Najeriya, inda farfesoshi masu cikakken aiki za su riƙa samun ƙarin Naira Miliyan 1.8 a shekara, yayin da masu karatun gaba masu cikakken aiki za su riƙa karɓar Naira Dubu 870,000 a shekara.

Sabon alawus ɗin yana ƙarƙashin tsarin da aka kira alawus na matakin farfesa, kuma yana shafar malaman jami’a da ke matakin farfesa da na karatun gaba ne kadai.

Alawus ɗin bai shafi sauran rukunin malaman jami’a ba, domin an ware shi ne musamman ga waɗanda ke matakan farfesa da karatun gaba a jami’o’in ƙasar.

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya sanar da wannan mataki a ranar Laraba a Abuja, a yayin gabatar da yarjejeniyar da aka sake tattaunawa tsakanin Gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Wannan alawus na cikin matakan da gwamnatn tarayya ta ɗauka bayan tattaunawa da ASUU kan batutuwan walwalar malaman jami’a.

A cewar sa, matakin yana daga cikin ƙoƙarin da ake yi na inganta yanayin aiki da jin daɗin malamai a jami’o’in Najeriya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here