Spain ta doke zakarun Turai, England da ci 1-0, inda ta zama zakarar gasar cin kofin duniya ta mata a wasan karshe da aka yi a filin wasa na Australia a Sydney a yau Lahadi.
Kyaftin Olga Carmona ce ta zura kwallo ɗaya tilo a ragar England tun a minti na 29 da fara wasa.
England ta samu damar farke kwallon ta hannun Lauren Hemp, wacce ta buga ƙwallo da ƙarfi amma sai ta doki ƙarfen taga.
Sai dai kuma an dakatar da wasan bayan da wani dan kallo ya barko cikin fili sanye da rigar ‘Free Ukraine’ kafin jami’an tsaro su cafke shi.