Ana ci gaba da gudanar da shari’a kan masarautar Kano

Kotu, Masarauta, gudanar, shari'a, Kano
A yau Alhamis babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta fara sauraron ƙarar da Aminu Babba Ɗan'agundi ya shigar gabanta inda yake ƙalubalantar matakin...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

A yau Alhamis babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta fara sauraron ƙarar da Aminu Babba Ɗan’agundi ya shigar gabanta inda yake ƙalubalantar matakin majalisar dokokin jihar ta Kano na rushe masarautu biyar, tare da cire Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin kano, da mayar da Muhammadu Sanusi II, a kan sarautar.

Dambarwar sarautar ta kai ga Muhammadu Sanusi na biyu, wanda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya mayar a kan karaga yake zama a gidan sarkin, tare da zama a fadar da ke ƙofar kudu, yayin da shi ma Aminu Ado Bayero ke zama a gidan sarki da ke unguwar Nassarawa.

Karin labari: Abuja Zuwa Kaduna: Hukumar NRC ta bayyana dalilin lalacewar wani jirgin kasa

Al’ummar Najeriya da dama musamman na jihar ta Kano sun zuba ido don ganin yadda za ta kaya ganin yadda mutanen biyu ke jayayya kan masarautar Kanon mai ɗumbin tarihi.

Saidai rahotanni sun nuna cewa an jibge jami’an tsaro a hanyoyin zuwa babbar kotun, inda Mai Shari’a Abdullah Muhammad Liman ke sauraron ɓangarorin Kotu Masarautada ke cikin wannan ƙara.

Kotu Masarauta

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here