Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN ta sanar da bude filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu daga ranar Litinin mai zuwa.
wa Da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar FAAN, Obiageli Orah, ya ce sake bude filin jirgin ya biyo bayan kammala gyaran titin jiragen sama na gaggawa.
“Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu, jihar Enugu, zai sake bude harkokin sufurin jiragen sama a ranar Litinin 28 ga Afrilu, 2025, bayan an kammala gyaran titin jirgin na gaggawa.
“A ranar 18 ga Afrilu, 2025, Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta sanar da cewa, sakamakon fashewar kwalta kwatsam a wani muhimmin sashi na titin jirgin, za a rufe titin jirgin domin gyaran gaggawa.
Karin karatu: Rundunar Soji ta musanta shirin fara daukar sabbin ma’aikata
“An shirya fara aikin ne a ranar 22 ga Afrilu kuma a kammala kafin a bude shi a ranar 6 ga Mayun 2025. Sai dai kuma an kammala aikin gyaran titin jirgin, kuma injiniyoyin da ke aiki da FAAN sun share titin jirgin domin sauka da tashi,” in ji Orah.
FAAN na jinjinawa duk masu amfani da filin jirgin da masu ruwa da tsaki bisa fahimtar da suka bayar da hadin kai a lokacin rufewar.
Hukumar ta kuma bayar da uzuri game da wannan matsala, tare da tabbatar wa jama’a cewa an dauki dukkan matakan da suka dace don kare lafiya.