Aminu Bala Madobi
Yawancin mutane suna sane ko kuma da alama sun manta cewa duk abin da ya kai kololuwa, galibi, wata rana zai yo ƙasa.
To, yanzu lokaci ya yi da za a kawo karshen balahirar yawaitar gudun hijira da tururuwar ficewa da ake samu a jam’iyyar APC a Kano.
Wannan al’amari ne da mai yiwuwa zai yi tasiri ga jam’iyyar mai mulki a babban zabe mai zuwa da za a yi a shekara mai zuwa.
Sai dai ga alama wani abu ne ya sakwarkwace tareda susucewa a wani wuri da ya sanya lissafin siyasar APC a Kano cikin Wannan Hali.
Tagomashi da karsashi da jam’iyyar APC ke cigaba da kwarara a jam’iyyar NNPP ta Sanata Kwankwaso ya yi a halin yanzu, da sauran jiga-jigan jam’iyya mai mulki a Kano wani lamari ne da mai yuwuwa ke nuna alamar rashin katabus da alama lokaci bai kasance a bangaren jam’iyya mai mulki a Kano ba don daukar matakan da suka dace na gaggawa don gyara matsalar, da ga dukkan alamu jam’iyyar ke gab da durkushewa.
Duk da haka, Allah ne kaɗai ya sani! Wannan gagarumin tasiri na raguwa da zaizayewa ya fara daukar hankali ne a lokacin da tsohon kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum da magoya bayansa suka jagoranci ficewa daga jam’iyyar. Yayin da Hon. Kawu Sumaila, Hon. Abdulkadir Jobe, Alhaji Ali Makoda, mataimakin kakakin majalisar dokokin Kano, da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar suka tattara kayansu na siyasa, suka fice abinsu zuwa NNPP, sabuwar jam’iyyar da ta tashi daga karkashin jagorancin shugaban akidar jajayen huluna akidar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Babban abin da ya jefa firgici a kashin bayan jam’iyya mai mulki shi ne labarin sauya sheka da Sanata Ibrahim Shekarau ya yi zuwa jam’iyyar NNPP.
Jin labarin cewa an kammala duk wani tuntuba, wanda hakan ya sa gwamnan jihar Kano mai barin gado ya garzaya ya kai ziyarar bazata fadar Mundubawa domin isar da sako ga Sardaunan Kano, cewa ana bukatar kulawar sa daga fadar shugaban kasa da ke Abuja cikin gaggawa.
Wani mataki da ke da ma’ana da matakin da ya kamata a dauka na ganin an tafka kura-kurai a jerin kura-kuran da ake yi wa jam’iyyar APC a Kano.
Wata alama ce ta wani sauyin sheka wanda da alama tsawa ta kusa rutsawa da jam’iyyar wadda ta fito daga dan takarar me saran a tsayar dashi kuma dan siyasa – Murtala Sule Garo.
An dai ce Garo yana ta nuni tareda zaburarwa ne saboda rashin zaban shi a matsayin dan takarar gwamna, maimakon mataimakin gwamna na yanzu, Alhaji Nasiru Gawuna wanda aka nada a matsayin dan takarar jam’iyya a zabe mai zuwa.
Kamar yadda rahotanni suka ce Garo ya ji takaicin Janye jiki tareda ficewar gwamna Ganduje kwatsam daga takararsa ta Sanatan Kano ta Arewa tare da mikawa babban abokin hamayyar sa Sanata Barau Jibrin.
Hakazalika, ya koka da yadda ake cin amanarsa bisa la’akari da irin gudunmawar da ya baiwa gwamnati daga shekarar 2015 zuwa yau.
Batutuwan da suka taru an ce sun harzuka Garo wanda ya yi barazanar ficewa zuwa ga wata jam’iyya.
Lamarin da ya sa Khadimul-Islam ya garzaya zuwa gidan Garo ya sa shi ya janye yunkurinsa na sauya sheka zuwa wata jam’iyya.
Rikicin sauya sheka da ya mamaye jam’iyyar APC a Kano, a cewar masana harkokin siyasa na nuni da mummunan tasirin da ba a iya misaltawa ba Wanda matsaloli ne birjik da Ake alakanta shi Gwamnatin ta tafka.
Amma, dangane da wannan ci gaba, akwai buƙatar yin wasu tambayoyi, tun da babu batun hayaki da zai tashi ba tare da wuta ba.
Ko mene ne dalilin da ya jawo tabarbarewa a jam’iyyar APC a Kano?
Shin gwamna, Khadimul Islam ba shi da masu ba shi shawara nagari ne da zai yi masa jagora wajen dakile wannan ta’asa ta rikidewa kafin al’amura su kau? Me ya sa Gwamna Ganduje ke tattaki wajan taka sayyadar sa zuwa wajen jiga-jigan jam’iyyar a lokacin da suke shirin shawarar ficewa daga jam’iyyar? Shin bai yi tunani ba game da sakamakon da zai biyo baya nan da nan? Ina lissafin siyasar APCn Kanon ya shiga ne dake kokarin kwancewa jam’iyyar zane a kasuwa?













































