Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘Yan kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC kan su guji sanya siyasa a cikin harkokinsu domin hakan ka iya ruguza kimar ‘yan kwadago a kasar nan.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja.
Ministan ya ci gaba da cewa, ma’aikatar sufurin jiragen sama ba ta da hannu a cikin zagin jami’an tsaro sun yi wa shugaban kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajero, duka tare da tsare shi.
Kiran Keyamo na zuwa ne a yayin wata zanga-zangar da aka yi a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, dake Abuja da sanyin safiyar Alhamis din nan.
Keyamo ya yi nuni da cewa zanga-zangar ta shafi baki da ke shigowa kasar nan daga kasashen waje da kuma ‘yan kasar da ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, domin a cewarsa, masu zanga-zangar sun dakile harkokin sufurin jiragen sama ta hanyar tare hanyar shiga filin jirgin Nnamdi Azikwe.
Tun bayan kama shugaban NLC Ajaero tare da dukansa, gwamnatin jihar Imo ta musanta cewa tana da hannu a ciki, ta kuma zargi shugaban kungiyar da shiga harkokin siyasa.
Ko da yake kungiyoyin sun dage cewa zasu shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan nan da muke ciki na Nuwamba, a fadin kasar nan.