Ofishin jakadancin Kanada a Najeriya ya ce har yanzu cibiyoyin neman biza dake Abuja da Legas na nan a bude ga jama’a.
Mai Magana da yawun ofishin Jakandancin na Kasar kanada Mista Demilade Kosemani, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ofishin ya fitar a ranar alhamis din nan, bayan tashin gobara a wani sashe na ginin ofishin da ke Abuja, tun a ranar Litinin din da ta gabata 6 ga watan Nuwambar 2023.
A cewar sanarwar ga ‘yan kasar ta Kanada a Najeriya masu bukatar taimako za su iya shigar da bukatar su ta shafinsu Internet wato (https://www.canada.ca/en/immigration-refugees citizenship/services/application/check-status.html).
“Ga ‘yan kasar Kanada a Najeriya wadanda ke bukatar taimakon gaggawa: zasu iya tuntubar sos@international.gc.ca ko +1 613 996 8885 ko ta manhajar whatsapp akan lambar waya +1-613-909-8881.”
Kamfanin Dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, tashin gobarar a wani sashe na ginin ofishin Jakadancin Canada da ke Abuja a ranar Litinin din da ta gabata ya hallaka mutane biyu ciki har da wani ma’aikacin yankin tare da jikkata wasu biyu.