Akantoci mata sun ƙaddamar da sabbin shugabanni a Kano

IMG 20220521 181054 193 678x381 1
IMG 20220521 181054 193 678x381 1

Ƙungiyar mata Akantoci ta Najeriya SWAN reshen jihar Kano, ta ƙaddamar da kwamitin zartaswa na farko, inda Misis Christiana Oluranti-Danladi, ta zama shugabar ƙungiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kwamitin mai mutane 11 ana sa ran zai jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru biyu.

Danladi ta ce, a zangon shugabancinta za ta tabbatar da cewa ta inganta harkokin ilimi, horaswa da ilimin kiwon lafiya ga mambobin ƙungiyar.

Haka kuma ta yi alƙawarin tabbatar da ganin cewa sun shiga cikin ayyukan bada gudunmawa da kuma tallafa wa al’umma.

A cewarta, za kuma su bada fifiko wajen ƙarfafa horas da matasa ta hanyar tattaunawa kan sana’o’in dogaro da kai da sauran hanyoyin ci gaban al’umma.

“Za mu gudanar da shirye-shiryen karfafawa mata gwiwa da kuma horas da su kan harkokin kuɗi, da sauransu,” in ji ta.

Tun da farko, tsohon shugaban cibiyar ƙwararru ta Najeriya ICAN kuma shugaban taron, Alhaji Isma’ila Zakari, ya taya sabbin zaɓaɓɓun shugabannin murna, ya kuma buƙace su da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ita kuwa shugabar SWAN ta Najeriya Misis Nwamara Nnaji, ta taya sabbin shugabannin kungiyar murna, inda ta buƙace su da su bi ka’idojin aiki musamman wajen yin gaskiya da riƙon amana.

Ta kuma bukaci matan akantocin da su jajirce wajen ganin an samar da zaman lafiya a Najeriya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here