Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi ‘Yan Nijeriya 129 dake gararamba a birnin Agadez dake jamhuriyyar Nijar, da yammacin ranar Asabar a birnin Kano.
Shugaban hukumar ta kasa dake kula da ofishin jihar Kano Dakta Nuraddeen Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labrai lokacin da yake karbar wadanda aka dawo dasu din.
Jaridar Solacebase ta bayyana cewa mutanen da aka dawo da su sun iso Kano ne a cikin wasu motocin Bus Bus guda uku da kungiyar kula da hijirah ta duniya ta shirya.












































