NDLEA ta kama ɗan Indiya da ’yan Najeriya uku da magungunan Tramadol na biliyoyin Naira a Legas

WhatsApp Image 2025 09 14 at 11.32.18 2 (1)

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta cafke wani ɗan kasuwa ɗan Indiya, Gupta Ravi Kumar, tare da wasu ’yan Najeriya uku Ogunlana Noah Olanrewaju, Olushola Idrees Kayode and Bakare Korede Muheeb bisa zargin shigo da ƙwayoyin tramadol sama da miliyan biyu (2,248,000) da aka kama a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Solacebase ta rawaito cewa, ƙwayoyin da darajarsu sun kai sama da Naira biliyan 3.9 an shigo da su daga Delhi, Indiya, an kuma ɓoye su a matsayin sinadarin multi-vitamins cikin katuna 114.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama direbobi biyu da mai clearing agent yayin da suke ƙoƙarin fitar da kayan a manyan motoci. Daga baya kuma an kama ɗan kasuwar Indiya lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kayansa.

A wani samame daban, jami’an NDLEA sun kama wani fasinja, Onyeganochi Stanley Ifeanyi, a filin jirgin sama na Legas, inda aka gano gram 900 na skunk da aka ɓoye a cikin ƙwaryar kifi.

Karin labari: NDLEA ta kama masu safarar miyagun ƙwayoyi, ta ƙwace hodar Iblis da kuɗin ta ya kai Naira Biliyan 5.3

Binciken ya kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Ohadiegwu Uchenna, wanda shi ne ya ba shi jakar.

Haka kuma, hukumar ta kwace wasu nau’o’in miyagun ƙwayoyi a Legas, ciki har da 81.7kg na Canadian Loud da 1.2kg hashish oil daga kwantena a tashar Tincan Port, da kuma methamphetamine da aka ɓoye a picture frame da video players a cibiyoyin aika kaya.

A Ikorodu kuma, an gano masana’antar hada skuchies inda aka kwace kwalabe fiye da dubu 6 da kuma tabar wiwi mai nauyin tan 4.

Bincike ya kuma kai ga kama wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi a Abuja, Kano, Oyo, Anambra, Yobe, Ogun da Edo, inda aka gano tarin tabar wiwi, tramadol, methamphetamine da sauran ƙwayoyi masu haɗari.

NDLEA ta ce tana ci gaba da ƙarfafa yaki da miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar don kare al’umma daga illolinsu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here