Birnin tarihi na Kano ya yi cike da murna da shagulgula a ranar Asabar wajen bikin zagayowar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), wanda aka fi sani da Mawlid Nabiyy ko Takutaha.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Dubban Musulmi maza da mata da yara sun taru a manyan tituna da wurare daban-daban na birnin, suna gudanar da jerin gwanon yabo tare da rera waƙoƙin yabo ga Manzon Allah.
Malamai sun gabatar da wa’azozi inda suka bayyana halaye na kirki da Annabi (SAW) ya yi fice da su, tare da ƙarfafa musulmi su kwaikwayi rayuwarsa ta tawali’u, zaman lafiya da tausayi.
Kungiyoyin masu biki sun rika yin jerin gwanon yabo dauke da tutoci da manyan takardu masu rubutu suna waka cikin nishadi a cikin titunan Kano.
Malam Abubakar Mohammed daga Unguwar Wanbai ya yi kira ga Musulmi da su ɗauki darasi daga rayuwar Annabi (SAW), yana bayyana shi a matsayin mutum na zaman lafiya, ƙauna, tawali’u da adalci.
Shi ma Malam Musa Isa daga Tarauni ya bayyana zagayowar ranar haihuwar Annabi a matsayin lokacin tunani da ƙarfafa imani, inda ya yi kira ga Musulmi su dage wajen bin koyarwar Musulunci.
Jama’a sun nuna farin ciki da yadda bikin ya gudana lafiya ba tare da wata matsala ba, yayin da jami’an tsaro suka yi ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro ta hanyar sintiri a wurare masu muhimmanci.
NAN













































