A ranar Asabar aka gudanar da bikin Gani na shekarar 2025 a garin Yashikra da ke ƙaramar hukumar Baruten a Jihar Kwara, inda manyan baki daga ciki da wajen Najeriya suka halarta.
Bikin gargajiya na shekara-shekara wanda ke haɗa ’yan asalin Yashikra a fadar Sarkin gari ya samu fitowar daruruwan mahaya da suka yi ado da kayan gargajiya, abin da ya nuna al’adun Yashikra na musamman.
A jawabin sa, Sarkin Yashikra, Alhaji Imorou Usman Sariki Sabi-Kpasi II, ya shawarci al’ummar Baruten da su rungumi ƙauna da haɗin kai domin samun cigaba.
Ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da na jiha wajen yaki da rashin tsaro, sai dai ya nemi ƙarin matakai masu ƙarfi domin kawo ƙarshen matsalar.
Har ila yau, Sarkin ya gargadi matasa da su guji shaye-shaye da amfani da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa hakan zai ba su damar amfani wa kansu da kuma al’umma.
Shi ma Sarkin Ilesha Baruba, Farfesa Halidu Abubakar, ya bukaci jama’a da su manta da sabanin juna, na mutum ko na ƙauyuka, domin su cimma ci gaban haɗin kai a yankin.













































