Gwamnatim tarayya za ta ciyar da dalibai miliyan 50 a 2026 – Mahukunta

Kaduna school feeding

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana shirin faɗaɗa shirin ciyar da Daliban Makaranta na ƙasa (NHGSFP) domin ya riski dalibai kusan miliyan 50 a makarantu na firamare a shekarar 2026.

Shugabar shirye-shiryen NSIPA, Dakta Aderemi Adebowale, ta ce shirin zai haɗa ɗaliban firamare daga aji ɗaya zuwa na shida da kuma yara marasa zuwa makaranta.

Ta bayyana cewa za a iya samar da abinci mai gina jiki ga ɗalibi a kan kuɗi na kusan Naira 500 a kullum.

Ta ƙara da cewa gwamnati tana aiki tare da manoma ƙanana, masu sayar da kaya da kuma abokan hulɗa don rage tsadar abinci ta hanyar daidaita farashi kai tsaye daga gonaki maimakon na kasuwa.

Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da rabon kayan aikin lafiya da magunguna da kuɗin su ya kai Naira biliyan 23 don farfaɗo da cibiyoyin lafiya a matakin farko

Adebowale ta ce wannan tsarin zai taimaka wajen tabbatar da tsadar abinci mai sauƙi da kuma ingantaccen biyan kuɗi da isar da hidima.

A ranar 27 ga Mayu, 2025, gwamnati ta ƙaddamar da shirin sabunta fata na ciyar da dalibai a Abuja domin ciyar da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta da kuma marasa galihu zuwa shekarar 2026.

Shirin yana daga cikin manyan tsare-tsaren Cibiyar tallafin Jama’a (NSIPA) da aka gabatar a wa’adin shugabancin Bola Ahmed Tinubu na biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here