Bayan da aka shafe watanni ana kai ruwa rana a batun yajin aikin ASUU, gwamnatin Buhari a ranar Talata ta ce tana iyakar kokarinta don ganin ta kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyar malaman jami’o’i.
Wannan na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Adamu Adamu a wata ganawa da ake yi da shugabannin jami’o’in tarayya da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a Abuja.
Ya zuwa yanzu dai da rahoton na nuni da cewa manyan jami’an na gwamnati suna cikin ganawar sirri. Ana sa ran minista Adamu zai yi wa manema labarai bayani da zarar an kammala ganawar.
Minista Adamu ya batu daga shugaba Buhari na kan matsayar cewa, duk da ana kokarin malamai su koma bakin aiki, amma ba za a maimaita kuskuren rubuta wata yarjejeniya da ba za ta haifar da da mai ido ba.
Karin bayani na nan tafe…