Dan kasar China, Mista Frank Geng-Quangrong, mai shekaru 47, a ranar Alhamis, ya sake shaida wa wata babbar kotun Kano cewa bai taba niyyar kashe budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani mai shekaru 22 ba.
Wanda ake tuhumar wanda ke zaune a Railway Quarters Kano ana tuhumarsa da laifin kisan kai.
Frank, wanda lauya mai kare shi, Mista Muhammad Dan’azumi ya jagoranta, yace ya bata kyautar Redmi bakar wayar hannu, sakonnin WhatsApp, hotuna, bidiyon mamaciyar.
“Cikin abubuwan da aka iya ganowa a gidan dake railway quarters yayin bajekolin sun haɗa da wayar wanda ake tuhuma, kwamfuta ta WhatsApp dakuma irin tattaunawa tsakanin Frank da Ummukulsum tsakanin Satumba 13 da Satumba 16, 2022.
“Sauran abubuwan da aka baje kolin sun hada da hotuna, karbar kayan adon gwal na Naira miliyan 5 da ya saya wa Ummukulsum da kuma bakar filashin 4GB mai dauke da bidiyon marigayiyar a gidansa,” inji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa faifan bidiyon da aka kunna a kotu, ya nuna marigayiyar tana wasa da karen, Charlie a gidan Frank da ke Railway Quarters Kano.
Yayin da yake yiwa wanda ake tuhuma tambayoyi, lauyan masu shigar da kara, babban lauyan Kano, Musa Abdullahi-Lawan, ya tambayi wanda ake kara inda yake kuma wa ya aiko masa da faifan bidiyon marigayiyar.
“Ummukulsum da alama tana cikin farin ciki sosai kuma tana raye a bidiyon, ta rasu a yanzu. Wa ya kashe ta?
“Ka shaida wa kotu a cikin shaidarka cewa a wannan rana ka kira marigayiyar ta waya amma ta ki dauka.
“Me yasa ka je gidan su ba tare da an gayyace ka ba?”
“A wannan rana mai muni sai tayi kira kiran WhatsApp ta ce in kawo ma ta karenta mai suna Charlie.
“Da isa gidanta, bayan ta ki amsa kirana, sai na aika mata da sakon tes, daga baya mahaifiyarta (Fatima Zubairu (Pw1)) ta bude gate, na shiga dauko Charlie.
“Ban yi magana da mahaifiyar marigayiyar ba saboda ba ta jin Turanci kuma ba na jin yaren Hausa,” in ji Frank.
Abdullahi-Lawan, ya yi zargin cewa wadda ake kara a ranar 16 ga Satumba, 2022 ya daba wa marigayiyar wuka a gidan su da ke Janbulo Quarters Kano.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, ya amince da shaidar kuma ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 29 ga watan Maris da 30 ga watan Maris domin ci gaba da kare kai da yi masa tambayoyi.













































