Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Juma’a sun kashe mutane 10 a kauyen Ta’agbe da ke masarautar Miango a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Uba Ogba, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a birnin Jos a ranar Juma’a.
Ogaba ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya ziyarci inda lamarin ya faru kuma ya tura karin jami’ai domin dakile tabarbarewar doka da oda a yankin.
A martaninsa kan lamarin, Danjuma Auta, babban sakataren kungiyar ci gaban yankin Iregwe (IDA), ya bayyana damuwarsa kan lamarin.
Auta ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an ceto rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce al’ummar Iregwe sun rungumi zaman lafiya kuma za su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.













































