Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce ta tuntuɓi hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa domin ganin ta gaggauta maido da ayyukan sadarwar da aka dakatar a wasu ƙananan hukumominta.
Solacebase ta rawaito cewa hukumomin tsaro sun buƙaci a rufe hanyoyn sadarwar a wasu yankuna tun a watan Oktoban da ya gabata, a wani mataki na magance ayyukn ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar ta bayyana cewa, yanzu haka hukumomin tsaro sun sanar da gwamnati cewa za a iya dawo da harkokin sadarwa.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana dawo da ayyukn sadarwar yau Juma’a a wani taron manema labarai.
Ya ce “Matakan da aka ɗauka na tabbatar da tsaro, musamman rufe hanyoyin sadarwa ya taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasarori kuma za su ƙara haifar da kyawawan sakamako ga jami’an tsaro nan ba da jimawa ba.”
”Tsawon aiki da wannan matakin ya kasance a koyaushe ba a cikin tambaya, saboda tasirinsa ga hallcin ayyukan ƴan ƙasa da kasuwanci” in ji kwamishinan.
“An shawarci mazauna yankin da cewa maido da cikakken ayyuka a yankunan da abin ya shafa na iya bayyana a cikin ƴan kwanaki, yayin da kamfanonin sadarwa ke yin ƙoƙarin ƙara i ga ta ayyukansu dai-dai da yadda ya dace.”
A cewar Arwan, gwamnatin jihar Kaduna ta yi ba ta ji daɗin yadda matsalar dakatar da ayyukan sadarwar ya shafi mutanen da yankunan da abun ya shafa.
Gwamnatin jihar na fatan yaba wa sadaukarwar da mazauna yankin suka yi yayin da wannan matakin na wucin gadi ya dade.
Haka ku. Aya ce, “Duk da haka, gwamnati na son sake jaddada cewa sauran matakan da aka sanar a matsayin wani ɓangare na umarnin tsaro na ci gaba da aiki, Waɗanda suka haɗa da haramcin amfani da babura masu ƙafa biyu a duk fadin jihar, hana kasuwannin mako-mako, safarar shanu, da kuma hana sayar da man fetur a jarkoki a ƙananan hukumomin da matsalolin tsaro ke faruwa.”













































