Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello za ta gudanar da taron lakcoci da ta saba gudanarwa shekara -shekara karo na 8 a jihar Kano, inda za’a gudanar da lacca mai taken “Reviving the Northern Traditional Institutions: Imperative for Peace and Security in Northern Nigeria”.
Solacebase ruwaito cewa ana gudanar da jerin lacca a kowace shekara inda masana, manazarta, masu tsara manufofi da masu ruwa da tsaki ke haduwa don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi batun ci gaban al’umma tare da samar da mafita a gare su.
A cewar wata sanarwa da Babban Daraktan Gidauniyar Engr Abubakar Gambo Umar ya fitar kuma aka aika wa Solacebase a ranar Laraba, Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo shine zai kasance babban bako na musamman, inda ake sa ran halartar Simon Bako Lalong, gwamnan jihar Filato kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin arewa, yayin da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai kasance babban mai masaukin baki.
Sanarwar ta ce taron zai gudana ne a dakin taro na Coronation dake fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Talata 18 ga watan Janairu, 2022.
‘’ Sarkin Lafia, Justice Sidi Bage (rtd) , shi ne zai kasance babban bako a wajen taron. Sauran fitattun ‘yan Najeriya da za su tattauna tare da samar da mafita kan batun sun hada da; Mai shari’a Ishaq Bello, tsohon babban jojin babban birnin tarayya Abuja, Farfesa Nancy Agbe, tsohuwar mataimakiyar shugabar jami’ar Mkar ta jihar Binuwai da kuma Farfesa Usman Abubakar na sashen nazarin kananan hukumomi da ci gaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria,” inji sanarwar.
Sannan kuma za a karrama fitattun mutane da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasa a wajen taron.










































