Buhari ya bayyana lokacin da Jiragin saman najeriya zai fara aiki

Nigeria air
Nigeria air

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Litinin din nan ya ce ana sa ran jirgin saman Najeriya zai fara aiki kafin karshen shekarar 2022.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake bayyana bude taron sake duba ayyukan ministoci karo na uku da aka shirya domin tantance irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufofin sa akan gwamnatin sa.

Ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da wannan aiki ne tare da bayar da takardar shedar tabbatar da filayen saukar jiragen sama na Legas da Abuja daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa, yayin da filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal ke gudanar da irin wannan tsarin ba da shaidar takaddar.

Ya bayyana irin ci gaban da aka samu ta fuskar noma, tattalin arziki, ababen more rayuwa, tsaro, lafiya, yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu.

Buhari ya shaidawa mahalarta taron da baki da suka halarci taron wanda ya hada da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta cewa an gina sama da kilomita 3,800 na hanyoyi a fadin kasar, yayin da aka sayo sabbin jiragen sama 38 ga rundunar sojojin saman Najeriya domin bunkasa aikin dan yaki da masu tayar da kayar baya.

Ya kara da cewa an yiwa ‘yan Najeriya sama da miliyan 38 cikakkiyar allurar rigakafin cutar COVID-19 wanda ke wakiltar kaso me girma a tsarin da Gwamnatoci suka tsara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here