Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana zaben dan Majalisar dokokin jihar Kano na ƙaramar hukumar Takai a matsayin wanda bai kammala ba.
Farfesa Usman Ibrahim na Jami’ar Bayero dake Kano, wanda shi ne jami’in dake tattara sakamakon zaben shi ne ya bayyana hakan a ofishin hukumar ta INEC da ke ƙaramar hukumar Takai.
A halin yanzu, INEC ta bayyana Malam Garba Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Ɗan Majalisar dokokin na mazabar Tsanyawa/Kuchi a jihar Kano.
Farfesa Ganiyu Shokobi na jami’ar Bayero, wanda shi ne jami’in dake tattara sakamakon zabe na mazabar Tsanyawa/Kunchi, shi ne ya bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaben ta INEC da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa.
Ya ce Gwarmai ya samu kuri’u dubu 31 da 471 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Malam Mohammed Ali na jam’iyyar NNPP, wanda ya samu kuri’u dubu 27 da 864.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Bello Abdullahi na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 136.
Hakazalika, INEC a ranar Lahadi ta bayyana sakamakon zaben mazabar Shanono/Bagwai.
Farfesa Ahmed Iliyasu na jami’ar Bayero ne ya ayyana Ibrahim Kundila na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u dubu 38 da 21 da ya bashi damar doke Musa Aliyu na NNPP wanda ya samu kuri’u dubu 29 da 983.













































