Tarin magoya bayan jam’iyyar Labour (LP) a yankin kudu maso yammacin Najeriya sun sauya sheka inda suka koma jam’iyyar APC domin mara baya ga dan takararta na shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu, a zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.
Wannan na zuwa ne bayan wasu sa’o’i da Bashir Bashir, wanda shi ne dan takarar mukamin gwamna a karkashin jam’iyyar ya gana da Bola Tinubu a Abuja.
Wannan koma bayan na zuwa ne kasa da sa’a 48 d Peter Obi ya kawo karshen yakin neman zabensa a Legas da sauran jihohi 35 na kasar.
Mambobin jam’iyar ta LP sun narkar da dukkan rassan jam’iyar zuwa cikin jam’iyyar APC yayin wani biki da aka yi a Akure babban birnin jihar Ondo.













































