Abdulaziz Umar Ganduje, dan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a Jihar Kano karkashin Jam’iyyar NDC.
SolaceBase ta rawaito cewa yanke shawarar sayan fom din neman takara a jam’iyyar alama ce dake nuni da wani sauyi a doguwar alakar iyalin Ganduje da APC, ya kuma nuna dawowa zuwa sansanin siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Abdulaziz na magana kan burinsa na siyasa da ganawar da ya yi da Kwankwaso, wanda hakan ya kara tabbatar da jituwarsa da kungiyar siyasar tsohon gwamnan.
NDC, wacce Kwankwaso ya koma kwanan nan bayan barinsa jam’iyyar ADC, ta ci gaba da jawo hankalin masu ruwa da tsaki na siyasa da magoya baya a fadin Jihar Kano.
Masu sharhi kan siyasa na ganin shigar Abdulaziz cikin neman ka iya kara zafafa fafatawar siyasa a kananan hukumomin, musamman gabanin babban zaben 2027, tare da tsammanin fafatawa mai zafi da dan takarar APC.












































