Matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya da ke cikin kuncin tattalin arziki da su fara kananan kasuwanci irin su sayar da kosai, masara gasashshiya da kuli-kuli a matsayin hanyoyin samun kudin shiga.
Ta ce ba su bukatar babban jari domin farawa kuma suna iya taimaka wa iyalai wajen fuskantar kalubalen tattalin arzikin kasar.
Ta bayar da wannan shawara ne bayan ta karbi matan gwamnonin jihohi 36 a Abuja, inda ta jaddada shirye-shiryen da ta ke yi na tallafi da bada jari, wanda ofishinta ke bayarwa domin taimakon ’yan Najeriya masu karamin karfi.
A cewar Matar Shugaban Kasar, ayyukan ta na mayar da hankali ne kan ba da tallafi kyauta maimakon bashi domin masu amfana su fara kananan kasuwanci ba tare da damuwar biyan bashi ba.
“Muna kokarin wajen kara wa jama’a karfi, kuma don fara kasuwancin kosai ba ya bukatar jari da yawa. Don fara gasa masara… wani ma ya ce game da tallafi, suna cewa kuli-kuli ma ba ya bukata da yawa. Ba mu ba su bashi ba, mun ba su shi a matsayin tallafi kyauta,” in ji ta.
Sanata Tinubu ta ce ofishinta na ci gaba da tallafa wa ’yan Najeriya ta hanyar shirye-shiryen tallafi daban-daban da aka tsara domin inganta rayuwa da tabbatar da dogaro da kai.
“Saboda haka muna karfafa ’yan Najeriya gwargwadon iko. Abin da ke hannuna, na bayar kuma ina ci gaba da bayarwa, kuma wadannan su ne abubuwan da muka yi,” in ji ta.















































