Majalisar Dattawa ta gabatar da kudirin hana ƴan Najeriya da aka samu da laifi a ƙasashen waje fasfo na tsawon shekaru 10

Passports

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kudiri a ranar Talata da ke neman hana wa ‘yan ƙasar da aka samu da laifi a ƙasashen waje samun fasfo na ƙasa na tsawon shekaru goma.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa kudirin, wanda Sanata Abubakar Bello daga yankin Arewa ta tsakiya (Niger North) ya dauki nauyi, yana neman gyara dokar Fasfo domin ƙara tsauraran hukunci ga ‘yan Najeriya da ke aikata laifuka a ƙasashen waje.

Manufar kudirin ita ce hana ayyukan ta’annati da rashin da’a da wasu ‘yan ƙasar ke aikatawa a ƙasashen waje tare da farfado da mutuncin takardar shaidar fasfon Najeriya.

A lokacin da ake tattaunawa kan kudirin, Sanata Onawo Ogwoshi, wanda ya wakilci mai gabatar da kudirin, ya bayyana cewa wannan doka tana da muhimmanci kuma wajibi, domin ya zo lokacin da Najeriya ke bukatar gyara barna da wasu ‘yan ƙasa ke yi wajen bata sunan ƙasar.

Majalisar ta ce, idan aka amince da kudirin gaba ɗaya, zai taimaka wajen tsarkake sunan Najeriya a idon duniya da kuma kare martabar ‘yan ƙasa masu bin doka.

Ana sa ran kudirin zai wuce zuwa majalisar wakilai don nazari kafin ya koma fadar shugaban ƙasa domin amincewa da shi a matsayin l doka.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here