Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa rashin daidaito da dorewar manufofin gwamnati shi ne babban abin da ke hana Najeriya samun ci gaba mai ɗorewa a fannin tattalin arziki da noma.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron haɗin gwiwa tsakanin hukumar kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) da Bankin raya Afirka (AfDB), wanda aka shirya a gefen taron tattalin arzikin Najeriya da aka gudanar a Abuja.
Taken taron shi ne: “Zuba jari a hanyoyin samar da abinci ta zamani a cikin mawuyacin yanayi.”
Sanusi ya ce babbar matsalar Najeriya ita ce rashin ci gaba da manufofi daga gwamnati zuwa gwamnati, inda ya zargi ma’aikatar gwamnati da gazawa wajen kiyaye tarihin tsare-tsare don dorewar gyare-gyare bayan sauyin mulki.
Ya tuna cewa a lokacin da yake gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya kaddamar da bincike kan sarkar darajar amfanin gona guda shida domin ƙarfafa lamuni ga manoma da jawo zuba jari a cikin harkar noma.
Amma, a cewarsa, wasu muhimman gyare-gyare, musamman na tumatir a Kano, sun lalace saboda rashin bin tsari da kyau da kuma zubar dokoki.
Sanusi ya jaddada bukatar gina ingantattun darajar noma da za su jawo hannun jari daga masu zaman kansu maimakon dogaro da kuɗin gwamnati kaɗai.
Ya ce, gwamnati ba ta da isasshen kuɗi don magance matsalar manoma gaba ɗaya, amma tana iya samar da yanayi da zai karfafa gwiwar masu zuba jari.
Ya kuma gargadi gwamnati da ta guji sauya manufofi akai-akai, musamman kamar yadda aka saki dokar shigo da kayan abinci kwanan nan, abin da ya ce ya sa manoma da masu zuba jari suka yi asara.
Sanusi ya bayyana cewa daidaiton manufofi na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da talauci, kawo ƙarshen rashin tsaro, da kuma gina tattalin arziki mai ɗorewa.
A nasa bangare, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce noma shi ne ginshikin tattalin arzikin Najeriya, inda ya bayyana cewa jiharsa na ƙoƙarin fadada noman zamani don rage asarar bayan girbi da ƙarfafa samar da abinci.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya jaddada cewa babu ci gaban noma idan ba a gyara tsarin iri ba, yana mai cewa mafi yawan manoma a halin yanzu suna shuka hatsi maimakon ingantattun iri.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire domin magance ƙanƙantar filayen noma a arewacin ƙasar, tare da ƙarfafa darajar noma ta hanyar sarrafa amfanin gona a cikin gida domin ƙara ƙimar tattalin arziki.
Wakilin kamfanin Olam Nigeria, Ade Adefeko, ya bayyana cewa kamfanin na zuba jari da dala miliyan 45 wajen kafa masana’antar sarrafa waken soya a Jihar Ekiti, don ƙara habaka darajar noma a ƙasar.










































