Hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gudanar da bikin ɗaga darajar jami’ai 29 zuwa sabbin mukamai a ofishin kwamishinan ‘yan sanda na jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Bakori ya ja hankalin sabbin jami’an da su ci gaba da riƙe gaskiya, ladabi da sadaukarwa wajen aiki, inda ya jaddada cewa ƙarin mukamin da suka samu ya zo da ƙarin nauyi da alhakin gudanar da aiki cikin kwarewa.
Daga cikin waɗanda aka ɗaga darajarsu akwai mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda biyu, manyan sufetanda 21 da kuma sufurtanda guda shida.
Bakori ya ƙarfafa jami’an da su nuna jagoranci na gari da kuma riƙon amana wajen fuskantar matsalolin tsaro da ƙasa ke fama da su.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa, manyan jami’ai, baƙi na musamman, wakilan kafafen yaɗa labarai da iyalan waɗanda aka ƙawata sun halarci bikin a Kano.













































