Amurka ta shirya tsaf don buga wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2026, yayin da ake sa ran shugaba Trump zai halarta

JF Centre 750x430

An kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da babban taron rarraba ƙungiyoyin gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a yi a ranar 5 ga watan Disamba a cibiyar John F. Kennedy da ke Washington DC.

Za a fara taron da ƙarfe 12 na rana agogon gabashin Amurka, wanda yake daidai da ƙarfe 6 na yamma agogon yammacin Afirka.

Wannan taro dai na ɗaya daga cikin muhimman lokuta da masoya ƙwallon ƙafa suka fi jira domin sanin ƙasashen da za su fafata da juna.

Wakilinmu da ya ziyarci cibiyar ta Kennedy a safiyar Laraba ya ba da rahoton cewa, ana ci gaba da samun yawaitar cunkoson jama’a da suka shafi gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, lamarin da aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a gasar ta Mondial, yayin da miliyoyin masu sha’awar kwallon kafa za su zura ido tare da yin tunkaho a bikin baje kolin abokan hamayyar da za su yi musayan kwazo da kungiyoyin da suka fi so.

‘Yan jarida na kasa da na duniya sun fara yiwa cibiyar kawanya domin neman alfarma, sama da masu sha’awar kwallon kafa biliyan 1.2 ne ake sa ran za su bibiyi taron ta kafafen yada labarai daban-daban daga sassan duniya.

An gudanar da gyare-gyare a cikin cibiyar ta yadda za ta dace da matsayin taron, tare da girke kayan aiki na zamani, alamomin cikin gida da aka yi wa tsarin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, da ɗora tutocin ƙasashen da suka samu gurbi a gasar da za a buga a Amurka, Kanada da Mexico.

Hakan ya haɗa da allunan bayanai na lantarki da aka riga aka kafa a wuraren shiga da abubuwan da aka tanada na musamman domin faranta ran mahalarta taron.

Gasar cin kofin duniya ta bana za ta kasance mafi girma a tarihi, wadda za ta ƙunshi ƙasashe arba’in da takwas.

A halin yanzu ƙasashe arba’in da biyu sun samu gurbin shiga, sauran shida kuma za su fafata a zagayen tantancewa.

Duk da cunkoson aiki a cibiyar, wakilinmu ya lura cewa yanayi ya kasance cikin natsuwa yayin da baki da ma’aikata ke gudanar da ayyukansu.

Fadar shugaban ƙasa ta Amurka ta tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump zai halarci taron, kuma ana sa ran zai jagoranci gudanar da rarraba ƙungiyoyin.

Majiyoyi sun nuna cewa zai karɓi sabon lambar yabo ta zaman lafiya da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta samar, wanda ke nuna rawar da ake ganin ya taka a fannoni daban-daban.

Ko a baya ma ya halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin kulob-kulob ta duniya da aka yi a New Jersey a watan Yuli 2025.

Filin wasa na Azteca da ke birnin Mexico City zai karɓi wasan buɗe gasar, yayin da filin MetLife da ke New Jersey zai karɓi wasan ƙarshe.

A wannan karo, za a bayyana cikakkun lokutan wasanni da wuraren buga su gobe bayan taron rarraba ƙungiyoyin saboda sabbin tsare-tsaren da ke tattare da wannan gasa mai faɗi.

Masu shirya cibiyar John F. Kennedy ta bayyana cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta biya kuɗaɗe masu yawa domin gudanar da taron, tare da ƙarin tallafin da ya ƙara darajar shirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here