Majalisar Dattawa ta amince da ba da Naira miliyan 50 ga iyalan malamai da sojojin da aka kashe a satar Oriire

Senate

Majalisar Dattawa ta amince da ba da gudummawar Naira miliyan 50 ga iyalan mutum 5 da suka rasa rayukansu yayin sace dalibai da malamai daga makarantu a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da gudummawar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Ya bayyana mutuwar a matsayin sadaukarwa mai girma a fagen yaki da rashin tsaro.

Ya yaba wa Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa samun nasarar ceto dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su bayan kwanaki 56 suna tsare.

Ya ce za a baiwa kowacce daga cikin iyalan malamai 2 da sojoji 3 da suka mutu a lokacin aikin ceton Naira miliyan 10.

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa an gano sunayen malaman da suka mutu masu suna Michael Oyedokun, wanda masu garkuwar suka sare masa kai yayin da suke tsare da shi da kuma Mr. John Olaleye, wanda bisa ga bayanin shugaban makarantar, aka harbe shi yayin harin da aka kai makarantar.

A bangaren sojoji kuma, an gano Lieutenant F.A. Isaac, Private Silas Musa da Sergeant Abena John Jerome, dukkansu sun rasa rayukansu a lokacin aikin ceto.

Akpabio ya ce an yi nufin bada wannan gudummawa ne domin tallafawa iyalan da ke cikin bakin ciki, tare da amincewa da sadaukarwar da mamatan suka yi a wannan mummunan lamari.

Ya ce wadanda abin ya shafa na daga cikin wadanda lamarin garkuwar da aka yi a ranar 15 watan Mayu ya shafa, inda aka sace dalibai da malamai daga makarantu 2 dake Karamar Hukumar Oriire.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here