Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa Jihar Kano ta himmatu sosai wajen tabbatar da nasarar Jam’iyyar APC a duka matakai a babban zaben 2027.
Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Gwamnan ya yi wannan sanarwa ne a wani taro da ya yi da jami’an gwamnati da aka zaba da wadanda aka nada, wanda aka gudanar a babban dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano.
Gwamna Yusuf ya ce Kano za ta jagoranci kasar wajen samar da kuri’u masu yawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
Ya ce gwamnatin APC a Kano na da dukan dalilan goyon bayan da take baiwa Shugaba Tinubu, inda ya bayyana sake zabensa a matsayin alhakin dukkan ‘yan jam’iyya da jami’an gwamnati.
Gwamnan ya umurci dukkan wadanda aka nada a gwamnatinsa wadanda ba su yi rajista a jam’iyyar APC ba su yi nan take.
Ya ce dukkan jami’an gwamnati da aka zaba ko aka nada dole ne su yi rijista da jam’iyyar kuma su yi duk abin da ya kamata wajen karfafa tsarinta kafin zaben 2027.
Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa na da kudirin tabbatar da cewa APC ta yi nasara a zaben shugaban kasa, na gwamna, ‘yan Majalisar Dokoki na Kasa, na Majalisar Dokokin Jihar da na kananan hukumomi.
Domin kara karfafa gwiwa ga masu rike da mukaman siyasa, Gwamnan ya amince da ba da filaye ga mataimaka a bangaren siyasa sama da 300, wadanda suka hada da Manyan Mataimaka na Musamman da Kanana.
Ya kuma amince da biyan Naira 100,000 ga kowane mai cin gajiyar.
Da yake jawabi a wurin taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya ce APC ba ta da wani dalili da zai hana aiki domin tabbatar da nasarorin Shugaba Tinubu a Kano.
Haka kuma, Shugaban APC na Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa “an zana layin fafatawa” da kungiyar Kwankwasiyya, yana mai bayyana tabbacin cewa APC za ta yi nasara a 2027.
A karshen taron, jami’an gwamnati da aka zaba da wadanda aka nada gaba daya sun nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Jami’an ma sun yi alkawarin kara karfafa wayar da kan jama’a a kauyuka da aiki tare domin tabbatar da nasarar APC a matakai a babban zaben 2027.













































