Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran Sabuwar Jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar a zaben 2027 a Jihar Kano.
Kwankwaso ya kuma bayyana tsohon Mataimakin Gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Sanatan NDC a Kano ta Tsakiya.
Kwankwaso ya yi wannan sanarwar ne da safiyar ranar Juma’a a gidansa da ke Kano jim kadan bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da magoya baya suka halarta.
Da yake jawabi a yayin taron, Kwankwaso ya ce NDC za ta bayyana ‘yan takarar sauran mukamai a duka matakai gabanin zaben 2027.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwa kan shirye-shiryen jam’iyyar da kuma hadin kai a tsakanin mambobinta, yana mai rokon su ci gaba da kasancewa tare da jajircewa wajen tabbatar da nasara a zabuka.
SolaceBase ta ruwaito cewa wannan ci gaba ana sa ran zai sake tsara yanayin siyasa a Jihar Kano yayin da manyan jam’iyyun siyasa ke kara karfafa shirye-shiryensu na zaben 2027.












































