APC ta dage zaben fidda gwanin gwamna na Kwara

IMG 20260521 WA0016 768x576 1 750x430

Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa ya dage zaben fidda gwanin gwamna a Kwara zuwa ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa shugaban APC na jihar, Mista Sunday Fagbemi, ne ya tabbatar da dagewar a Ilorin yayin zaben fidda gwani da ake gudanarwa a ranar Alhamis.

Fagbemi ya ce shugabancin jam’iyyar na kasa ne ya umurci a dage zaben, duk da cewa ba a bayar da dalili ba.

“Babu cikakken bayani kan soke zaben banda cewa tawagar da ta fito daga ofishin kasa ta zo ta umarci a gudanar da zaven gobe,” in ji shi.

A halin yanzu, an ruwaito cewa ‘yan takarar gwamna guda takwas sun janye wa Amb. Abdulfatai Yahaya Seriki, wanda shi ne magajin da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya fi so, a ranar Alhamis.

Wannan ya biyo bayan shawarar da aka yanke bayan wata ganawa da aka yi da yammacin Laraba tare da Seriki da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

‘Yan takarar da suka bayyana goyon bayansu ga Seriki su ne: Dr Salako Oluwatoyin, Capt. Ahmad Mahmoud, Prof. Wale Sulaiman, Dr Mohammed Bio, Dr Toyin Alabi, da Hajiya Aisha Patigi.

Sauran su ne Sanata Ibrahim Oloriegbe da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu.

An ce ganawar ta kare da daukar alkawarin hadin kan jam’iyya, gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana da ci gaba da shirye-shiryen gwamnatin AbdulRazaq.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here