Gwamna Yahaya ya samu tikitin Sanatan Gombe ta Arewa

Inuwa Yahaya of Gombe.jpeg
Inuwa Yahaya of Gombe.jpeg

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC na Sanatan yankin Arewacin Gombe a zaben a 2027.

Jam’iyyar APC ta kuma ayyana Ahmed Muhammed da Jerry Damara a matsayin wadanda suka dauki tutar jam’iyyar a zaben Sanatan Gombe ta Tsakiya da Gombe ta Kudu.

Yahaya ya samu nasarar ne bayan samun kuri’u 131,009 a zaben fidda gwanin kai tsaye da jam’iyyar ta gudanar, yayin da Muhammed ya samu kuri’u 89,450, Damara kuma ya samu kuri’u 56,687.

Labiru Kafur, Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwani na APC, ne ya sanar da sakamakon a ranar Talata a Gombe.

Ya ce an gudanar da zaben ne a ranar Litinin cikin lumana da gaskiya tsakanin mambobin jam’iyyar masu katin shaida, bisa ka’idojin jam’iyyar.

Kafur ya ce an mika sakamako daga rumfunan zabe zuwa cibiyoyin tattara sakamako da aka ware a mazabu uku domin kammala tattarawa da sanarwa.

Ya ce an sanarwar da sakamakon yankin Gombe ta Arewa a sakatariyar Karamar Hukumar Kwami, na Gombe ta Tsakiya a sakatariyar Karamar Hukumar Akko, sai kuma na Gombe ta Kudu a sakatariyar Karamar Hukumar Kaltungo.

Shugaban ya ce ‘yan takarar sun cika sharuddan doka kuma sun samu mafi yawan ingantattun kuri’un da aka kada a yankunansu.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here