Ni amintaccen ɗan jam’iyyar APC ne — Buhari

Buhari APC NEW

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada sadaukarwarsa ga jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce zai ci gaba da biyayya ga jam’iyyar.

Buhari ya ce shi dan jam’iyyar APC ne mai biyayya kuma ba zai taba juya wa jam’iyyar baya ba.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun sa ya fitar a X ranar Alhamis, 13 ga Maris, 2025.

Kalaman na Buhari ya zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa a kan shirin hadin gwiwa tsakanin ‘yan siyasa masu sauya sheka da na adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Karin karatu: Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SDP – El-Rufai

Idan dai za a iya tunawa, bayan ficewar Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC da kuma sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ya ce ya tuntubi Buhari kuma ya albarkaci sauya shekarsa zuwa jam’iyyar adawa.

A wata hira da BBC Hausa, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya ce, “Na tuntubi Buhari kafin na bar APC a ranar Juma’a na je na same shi don yin shawara. Na ce masa ya yi mini addu’a, ya kuma sa min albarkarsa.”

Sai dai kuma tsohon shugaban kasar ya sake jaddada matsayinsa na zama a jam’iyya mai mulki, yana mai cewa zai so ya ci gaba da zama a matsayinsa na dan jam’iyya mai mulki mai aminci.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa da irin goyon bayan da jam’iyyar ta ba shi a baya da kuma lokacin da yake shugaban kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here