An ƙayyade wuraren sayar da burodi da man fetur a Zamfara

Zamfara, Dauda Lawal, man fetu, burodi
Zamfara Gov. Dauda Lawal

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan dokar haramta sayar da biredin da ba shi da sunan kamfani da wanda ake naɗewa cikin leda da kuma sayar da fiye da lita 50 na man fetur da kuma amfani da gilashin mota mai duhu a jihar Zamfara.

Gwamna Lawal ya sa hannu kan dokar ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Gusau.

Karin labari: Akwai shirin tura jami’an tsaron Kenya zuwa Haiti – Ruto

Wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce dokar ta yi maganin matsalolin da aka bayyana suna janyo ƙalubalen tsaro a jihar.

Ya ce an yi dokar ne saboda hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan wasu yankuna a sassan jihar.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun sake kai hari Kajuru tare da sace mata 7

Sanarwar ta bayyana cewa “sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan a wasu yankuna da ke sassan wasu ƙananan hukumomin jihar musamman Zurmi da Shinkafi da Ƙaura Namoda da Talata Mafara da kuma dawowar ayyukan ƴan bindiga da sace-sacen mutane a wasu yankuna da wasu manyan tituna a jihar.

Gwamnan ya kuma haramtawa masu motoci a jihar Zamfara amfani da gilashi mai duhu sannan kuma an haramta musu rufe lambar motocinsu a lokacin tuƙi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here