Barau, Akpabio da Kalu sun fara neman kujerar shugaban majalisar dattawa

Senate
Senate

Bayanan da aka samu daga wajen hukumar INEC ya tabbatar da cewa an samu sakamakon zaben ‘yan majalisar dattawa 98 a cikin 109. Vanguard ta ce jam’iyyu bakwai su ke da wakilci a majalisar amma a duka majalisun tarayyar, jam’iyyar APC ta ke da rinjaye da kujeru 57 da kuma 162.

Hakan yana nufin shugabancin majalisa ya na hannun jam’iyyar APC, kuma ta kai an fara shirye-shiryen wadanda za su rike mukamai a wannan karo.

Ba da dadewa ba ake sa ran jam’iyya mai-ci za ta fitar da yadda za a kasa kujerun majalisa. Za a ware kujeru zuwa wani yanki domin ayi adalci.

Tun da Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shetima sun fito daga Kudu maso yamma da Arewa maso gabas ne, za a raba sauran mukaman ga wasu bangarori.

Rahoton ya ce shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa a yanzu haka, yana cikin wadanda suka kwallafa rai a kan kujerar shugaban majalisar.

Sannan akwai Sanata Goodwill Akpabio daga Kudu maso kudu da ya fara neman kujerar.

Tsohon Gwamnan ya rike Ministan Neja-Delta a mulkin APC.

A majalisar wakilai, Hon. Aliyu Betara wanda ya lashe zabe a karo na biyar yana harin kujerar. Sai dai wasu na ganin mukamin na Arewa maso yamma ne.

Idan daga Arewa maso yamma za a samu shugaban majalisar wakilai, irinsu Hon. Alhassan Ado Doguwa sun ci buri, sai dai yanzu yana tsare a gidan yari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here