NDC ta kafa kwamitin mutum 17 da zai tantance ‘yan takara

NDC NDC

Jam’iyyar NDC, ta kafa kwamitin tantancewa mai mutum 17 domin tantance ‘yan takara da ke neman tikitin jam’iyyar na zaben Shugaban Kasa, Gwamna, Sanata da Majalisar Wakilai gabanin zaben fidda gwaninta.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakatarenta na Kasa, Barrista Ikenna Morgan Enekweizu ya fitar, inda ya ce an kaddamar da kwamitin da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Talata, 19 ga Mayun 2026.

Sanarwar ta ce an nada tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi kuma tsohon Sanata, Sam Egwu, a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Lauyan Jam’iyyar na Kasa, Barrista Reuben Egwuaba, zai yi aiki a matsayin sakatare.

Sanarwar ta ce kwamitin ya kunshi shugabannin jam’iyya, kwararru da mambobin Kwamitin Aiki na Kasa, NWC.

Sauran mambobin sun hada da Kwamared Babatunde Ali (Mataimakin Shugaba), Alhaji Buba Galadima, Hon. Mohammed Sani Takori, Mista Daniel Onifade, Mista Ikeddy Isiguzo, Mista Wole Adedayo, Dr. Osusu Osusu, Chief Asukewe Ikoawaji, Farfesa Udenta Udenta, Barrista Frederick E. Owotorufa, Hannatu Tanko, Mista Dogo Shammar, Sir Henry Obaze, Mista Clement Agiagie da Barrista Fatima Musa Abba.

Jam’iyyar ta ce kwamitin zai kasance da alhakin tantance dukkan ‘yan takarar da ke neman tsayawa takara karkashin tutar NDC gabanin zaben fidda gwani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here