APC a Kano za ta mara wa Tinubu da Abba baya su yi tazarce, ta kuma jaddada bin tsarin cikin gida kan sauran tikitai

IMG 20260501 WA0003 750x430

Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar Kano sun bayyana goyon bayansu a hukumance ga Bola Ahmed Tinubu a takarar shugabancin kasa na shekarar 2027 tare da amince wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa’adi na biyu.

Amincewar ta faru ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, inda tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya mika fom din nuna sha’awar tsayawa takara ga gwamnan.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa wannan ya nuna cewa jam’iyyar a Kano ta daukar Abban a matsayin dan takarar gwamna da jam’iyyar ta fi so.

Duk da amincewar, shugabannin jam’iyyar sun bayyana karara cewa ba za a bai wa sauran masu neman takara tikiti kai tsaye ba.

Sun jaddada cewa duk sauran mukaman za a yanke hukunci a kansu ta hanyar tsarin cikin gida da aka kafa, musamman ta hanyar shawarwari na bai daya.

Yayin da yake mika fom din, Ganduje ya ce shugabannin jam’iyyar sun riga sun amince da matakin goyon bayan Abba.

Ganduje ya cewa fam din nuna sha’awa da na tsayawa takarar gwamnan, wajibi ne a cike akan lokaci sannan a mika su bisa ga ka’idojin jam’iyya.

A halin yanzu, kudirin amincewa da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa tilo na jam’iyyar, Rabiu Sulaiman Bichi ne ya gabatar da shi kuma ya samu goyon bayan daga dukkan mahalarta taron.

Tun da farko, Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa sashen jihar ya shirya sayen fom fin tsayawa takarar Tinubu a matsayin nuna biyayya. Sai dai, a cewarsa wasu sun riga sun saya kafin su.

Taron ya sake tabbatar da hadin kan jam’iyyar gabanin zaben 2027 yayin da ya bar kofar gasa a bude ga sauran mukaman da ake takaddama a kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here