Hukumar kula da harkokin Shari’a ta Kano JSC ta amince da sabbin naɗe-naɗe, tare da janye dakatarwar da ta yiwa wasu

Kano CJ Dije Aboki 750x430

Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Kano (JSC) a karkashin shugabancin Babban Jojin Jihar Kano Mai Shari’a DIje Abdu Aboki, a taronta na 79 na watan Fabrairu 2025, ta amince da nadin wadansu mutane da za su tallafawa hukumar wajan gudanar da aiyukanta.

Wadannan nade naden anyi su ne bayan la’akari da yin amfani da bayanai da kuma yadda suke gudanar da aikinsu da tawali’unsu da sadaukarwar don ganin ci gaban hukumar shari’a.

Waɗanda aka nada sune: Chief Magistrate Hajara Garba Ahmad a Matsayin Mukaddashin Babban Magatakarda na Babbar kotun Jihar Kano wato Ag Chief Registrar Sannan akwai Musa Ibrahim Umar Wanda aka nada Matsayin Mukaddashin Mataimakin Babban Magatakarda Mai kula da Harkokin mulki da ayyuka na musamman.

Sauran sune: Usman Adam wanda aka nada Matsayin Mukaddashin Mataimakin babban Magatakarda Mai kula da Harkokin Alkalan Majistare da Kuma Sakatariyar Cif Joji Fatima Garba Yakasai a Matsayin Mukaddashin Mataimakin Babban Magatakarda Mai kula da Harkokin shari’a.

Karin karatu: Kotu ta dage shari’ar zargin almundahana akan Ganduje zuwa watan Fabrairu 

Hakazalika akwai Chief Magistrate Hadiza Rabiu Bello wanda aka nada Matsayin Mukaddashin Darakta Bangaren Kula da ma’aikatan shari’a na Jihar Kano JSC da Chief Magistrate Zuhura Madaki a Matsayin Mukaddashin Darakta Bangaren Horaswa da Kuma babban Magistrate Malikatu Muhd Nuraini a Matsayin Mukaddashin Mataimakin Darakta Bangaren horawa.

Bugu da ƙari, hukumar ta JSC a dai wannan taron data gudanar ta tattauna akan dakatarwan da aka yiwa wadansu ma’aikatan kotu a watannin baya Inda ta yanke hukunci a kan dakatarwan da aka yiwa Bilya Abdullahi da Auwalu Ibrahim Khalil da Isma’ila Garba biyo bayan korafi da wani mai suna Muzdalifa ya Shigar dangane da zargin su da yin takardar umarnin kotu ta babu.

Sai dai bayan bincike mai zurfi da kwamitin karbar korafe korafe na hukumar JPCC yayi tare da mika rahoton sa ga hukumar yan sanda, su kuma sun mika sakamakon binciken su zuwa ofishin daraktan gabatar da kararraki na ma’aikatar shari’a ta Jihar Kano DPP inda daraktan ya bada shawarar cewa babu isasshun hujjoji da za su sa a samesu da Laifi.

Bisa ga waɗannan binciken, hukumar ta yanke shawarar janye dakatarwan da aka yiwa wadannan jami’an da aka ambata sunansu a sama, yayin da shi Bilya Abdullahi aka yi masa gargadi mai ƙarfi kan ya guji jefa kansa cikin haramtattun abubuwan da suka saba da dokoki da tarbiyar tafiyar da aiki.

A cikin wani al’amarin kuma na daban, hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Kano (JSC), a taronta na 79 Wanda aka gudanar Ranar 6/02/2025 tayi bitar dukkanin sakamakon binciken da kwamitin karbar korafe korafe JPCC yayi dangane da korafin da Alhaji Sani Bozo Rimin Gado yayi akan hudu Idris, Magatakarda a kotun Upper Shari’a Court dake garin Gwarzo da kuma Abba Bala Gwarzo Maigadin wacin Gadi a dai kotun ta Gwarzo.

Korafin da aka yi kansu shi ne tsoratarwa tare da karbar kudadan cin hanci.

To biyo bayan zuzzurfan bincike da kuma bayyanar waɗanda ake zargi a gaban kwamitin na JPCC tare da amsawar da suka yi da bakinsu na cewa suna da hannun cikin badakalar karbar cin hancin Naira dubu dari 214,000.

A cikin aniyarta tare da sadaukar da kai don tabbatar da Martaba da amincin shari’a, a jihar Kano, hukumar kula da harkokin shari’a ta tabbatar da shawarar kwamitin JPCC juma ta dauki wannan matsayi kamar haka:

Na farko shi Hudu Idris an rage masa mataki daya daga cikin matakan da ya taka a aiki, an sanya shi yin ritayar dole nan take saboda karbar cin hanci.

Yayin da aka janye kwantiragin Abba Bala Gwarzo nan take saboda rawar da ya taka wajan badakalar cin hanci.

Hukumar ta ce, ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajan tabbatar da bin doka da odar da kuma tabbatar da da’ar ma’aikatan shari’a domin samun amincewar jama’a a cikin tsarin gudanar da Shari’a, kamar yadda wata sanarwa da Baba Jibo Ibrahim mai magana da yawun Kotunan Jihar Kano a Madadin hukumar kula da harkokin shari’a ta Jihar Kano JSC ya fitar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here