Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bisa umarnin shugaba Bola Tinubu, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA) da za a gudanar a birnin New York, Amurka.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Mista Stanley Nkwocha, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa zaman na UNGA zai gudana daga Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28 ga Satumba.
Nkwocha ya bayyana cewa Shettima zai halarci taron bikin cikar Majalisar Ɗinkin Duniya shekaru 80 a ranar Litinin 22 ga Satumba, a hedikwatar MDD da ke New York.
Haka kuma, zai shiga cikin manyan baki a muhawarar taron daga ranar Talata 23 zuwa Lahadi 28 ga Satumba.
A madadin Shugaba Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa zai gabatar da jawabin Najeriya a ranar Laraba 24 ga Satumba, tsakanin ƙarfe 3 na rana zuwa 9 na dare agogon New York.
Har ila yau, zai halarci wani taro na musamman kan sauyin yanayi da sakataren ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a ranar 24 ga Satumba daga ƙarfe 2 na rana zuwa 6 na yamma, inda ake sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin tsare-tsarenta na NDCs ƙarƙashin yarjejeniyar Paris.
Bugu da ƙari, Shettima zai halarci babban taron zagaye na “Global Champions on Adequate and Affordable Housing” da shugaban ƙasar Kenya zai jagoranta a ranar 24 ga Satumba, tare da gudanar da wasu tarukan ƙetare da na musamman.
Bayan kammala taron UNGA, Nkwocha ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa zai zarce zuwa birnin Frankfurt na ƙasar Jamus domin ganawa da jami’an bankin Deutche Bank kafin dawowarsa Najeriya.
(NAN)













































